Thursday, June 22, 2017

Dino Melaye zai bar Majalisa ba girma ba arziki


An kai mataki na gaba wajen shirin maido Sanata Dino Melaye gida



  • Maganar tsige Dino Melaye daga Majalisa na ta kara karfi
  • Sanatan na Jihar Kogi na cikin babban matsala a halin yanzu
  • Melaye dai yace Gwamnan Jihar sa da wannan danyen aiki


Shirin kiranye: Cikin Sanata Dino Melaye ya duri ruwa


Dama kuna da labari cewa Dino Melaye na cikin tsaka mai wuya. Mutanen mazabar sa na Yammacin Kogi na shirin yi masa kiranye. Idan hakan ya tabbata Sanatan zai bar Majalisa ba girma ba arziki. 

Sanata Dino Melaye na Yammacin Jihar Kogi ya tare su bayan da Hukumar zabe ta kasa watau INEC ta karbi takardun shaida na cewa mutanen mazabar na Jihar Kogi sun zabi a maido Sanatan da su ka zaba gida.




Dama kun dai ji cewa mutane 188,588 su ka sa hannu inda su ka nemi a maido Sanata Dino Melaye gida daga Majalisar Dattawa inda yake wakiltar mazabar sa ta Yammacin Kogi. Kawo yanzu an mikawa Shugaban Hukumar zabe na kasa wannan bayani a jiya.

Rikicin Gwaman Bello na Jihar da Sanata Dino Melaye ya kai inda ya kai. Sanatan ya zargi Gwamnan Jihar da hannu a cikin yunkurin da ‘yan mazabar sa ke yi na yi masa kiranye wanda yanzu maganar tayi nisa. A baya dai an san Sanatan da yawan shiga cikin rikici ko yanzu ya za a kare?

           
[NAIJ Hausa]

1 comment:

  1. Dino Melaye: Zai bar majalisa ba girma" suggests Dino Melaye's aspirations for political office. Does Quality Affect This phrase hints at his potential candidacy, indicating his intention to contest elections and possibly join legislative bodies.

    ReplyDelete

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...