Goron Azumi: Falalar I’itikafi a cikin watan Ramadan
- Musulmai na
azumi a fadin Duniya a cikin wannan wata
- Akwai matukar lada ga wanda ya
kebe a masallaci
- Wannan kebewar
ake kira I’itikafi a Addini
Akwai matukar lada ga wanda ya samu yin I’itikafi a
cikin wannan wata. Manzon Allah SWT ya kan zauna a cikin masallaci yayi
ta ibada. Ana so Musulmai su yi koyi da wannan ibada na Manzon
Allah.
Yayin da ake azumin watan Ramadan yana daga cikin
ayyukan lada shiga I’itikafi watau kebawa a Masallaci ba a wani aiki face
salloli da karatun Al-kur’ani mai girma. A cikin Bukhari ya tabbata cewa Manzo
SAW na yin I’itikafi a irin wannan lokaci na karshen Ramadan.
Akwai Hadisi daga Abdullahi ‘Dan gidan Abbas RA daga
Manzo SAW da ke cewa duk wanda yayi I’itikafi a kwanaki goma na karshen Ramadan
ba zai shiga wutar Jahannama ba. Wannan Hadisi dai Imam Tabarani ya kawo shi.
Ana shiga I’itikafi ne cikin watan Ramadan wanda aka
fi ba karfi musamman a kwanaki goma na karshe. Sunnah ta tabbatar da cewa an fi
so a shiga I’itikafi kafin rana ta fada kuma a fito da zarar an ce an ga wata
watau kafin a shiga watan Eid.
Ana kuma I’itikafi ne a kowane Masallacin da ake
Sallar Juma’a watau ba sai mutum ya fita domin zuwa Masallaci ba. Akwai dai
Malamai irin su Nasir-Deen Albani da ke ganin Annabi SAW ya kayyade ga
Masallatan nan uku mafi maraja.
[Muhammad Malumfashi ya fara rubuta wannan a NAIJ Hausa a matsayin goron Jumu'a]
No comments:
Post a Comment