Tuesday, June 13, 2017

Gwamnati na shirin haramta Niqabi


Nikabi na hana Dalibai daukar darasi a Makaranta



– Ana yunkurin haramta Hijabi a Kasar Norway

– Masu amfani da nikabi za su fuskanci barazana

– Haramcin dai zai shafi kaf daliban makaranta





Kasar Norwegia za ta hana Jama’a sa nikabi. A jiya Gwamnatin kasar ta fara shirin kawo wannan doka. Nikabin na hana dalibai daukar karatu Inji Ministan Ilmi da bincike na Kasar.

Gwamnatin Kasar Norway na shirin haramta amfani da nikabi a Makarantun firamare da sakandare da ma na gaba da su. Gwamnatin na kukan cewa irin wannan sutura na hana dalibai fahimtar karatu da kyau.

Ministan Ilmi na kasar Torbjorn Roe Roe Isaksen ya bayyana wannan a jiya Litinin. Ana dai shirin kafa dokar da za ta haramta amfani da nikabin da ke rufe fuska nan da zuwa shekara mai zuwa wanda wannan dai na iya kawo rikici da Musulman kasar.




[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...