UCL: Ka ji abin da Gwamnan Ribas
yayi bayan Real Madrid sun yi nasara
– Kungiyar Real Madrid ce ta lashe
kofin Champions league na bana 2017
– Hakan ta sa
Gwamna Nyesom Wike ya hada ‘yar liyafa
– Gwamna Wike da
wasu ‘Yan PDP sun yi bikin murna
- Real Madrid ta doke Juventus a wasan karshe na kofin Champions league
- Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas yayi walima don murna
- Gwamnan zai kuma bude makarantar koyon kwallo na Real Madrid
Babban Dan wasan Real Madrid watau Ronaldo ya zura
kwallaye biyu a wasan su da Juventus a wasan karshe na makon. Juventus
ta sha kashi ne a hannun Madrid da ci 4-1 a Birnin Cardiff wanda hakan ta sa
Gwamna ya kira walima.
Gwamnan
Jihar na Ribas ya hada walima domin Jama’a su taya sa murnar lashe wannan kofi.
An ga Gwamnan tare da rigar Kungiyar Real Madrid da kuma mai dakin sa suna ta
faman murna bayan Kungiyar ta doke Juventus ta ajiye tarihi.
Ku
na sane cewa Real Madrid ta kara lashe kofin Nahiyar Turai na UEFA Champions
league inda ta lallasa Zakarun Italiya. Dan wasa Ronaldo ne ya kara gamawa da
kwallayen da su ka fi na kowa bayan ya jefa 2 a wasan karshe.
No comments:
Post a Comment