Idan Buhari ba ya nan, bai
dace Osinbajo ya zarce ba… Inji Okupe
– Doyin Okupe yana nan kan bakan sa game da zaben
– Okupe
yace ba a kyautawa ‘Yan Arewa idan Osinbajo ya zarce ba
– Dr. Okupe yace haka aka yi da
Jonathan bayan rasuwar Shugaba ‘Yaradua
‘Dan Arewa zai tsaya takara a 2019 ba Osinbajo ba Inji Okupe
Okupe ya kara jaddada
cewa Arewa ya dace ta tsaida dan takara idan Buhari ba ya nan. Na kusa da Shugaba
Jonathan din yace ba ayi wa Arewa adalci ba. Yanzu haka dai Osinbajo
ke rike da Najeriya bayan da Shugaba Buhari ya koma asibiti.
Babban mai ba shugaba Goodluck
Jonathan shawara a baya ya kara magana game da zaben 2019 inda yace bai dace Farfesa
Yemi Osinbajo ya zarce ba idan Shugaba Buhari ba zai tsaya ba ko wani abu ya
same sa.
Dr. Doyin Okupe yace
wasu ‘Yan Arewa na ganin cewa ba ayi masu daidai ba lokacin da Jonathan ya
zarce bayan rasuwar Shugaban kasa Ummaru ‘Yaradua. Okupe yace duk da ba dokar
da za ta hana Osinbajo tsayawa amma adalci shi ne ya ba Arewa wuri.
Ganin
yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke fama da rashin lafiya kuma bai bayyana
cewa zai tsaya takara ba. Tun kwanaki Doyin Okupe yace bai kamata kujerar ta bar
Yankin Arewa ba.
No comments:
Post a Comment