Abin
kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida
- Kasar Saudi ta aikowa Najeriya
sadakar dabino na azumi
- Sai ga shi yanzu ana saida wannan dabino a kasuwa
- Ministar kasar da tayi alkawarin
za a rabawa ‘yan gudun hijira
Wannan
abin kunya sai ace da me yayi kama. Najeriya
dai ta kara buga abin kunya a idon Duniya bayan an fara saida dabinon sadaka a kasuwa. An dai aikowa Najeriya sadaka amma an kai kasuwa domin a ci riba.
Kwanakin
baya kun ji cewa Ofishin Jakadancin Saudiya a Najeriya ya bayyana cewa kasar ta
aikowa Najeriya tulin dabino domin buda baki. Sai dai yanzu haka wannan dabino
na yawo a kasuwa cikin Abuja ana saidawa.
Karamar Ministar
harkokin kasar waje Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim tayi alkawari da fari
cewa za a raba kayan ne musamman ga ‘Yan gudun Hijira da ke Yankin Arewa maso
gabas sai dai ba haka abin ya kasance ba.
Gwamnatin
Tarayya ta bakin Ma’aikatar harkokin kasar wajen ta ba Kasar Saudiya hakuri
inda tace wasu bata-gari ne su ka yi gaba da dabinon bayan an kai inda ya
kamata a raba su domin su samu abin Duniya.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment