Sunday, June 18, 2017

Ikon Allah: Har da Patience Jonathan za a tsaya takara mai zuwa?



Dole na mu yayi: ‘Yan Kudu sun fito da ‘Yan takara a zaben 2019



– Inyamuran Najeriya sun fitar da ‘Dan takara a zabe mai zuwa


– Cikin wanda ake nema su tsaya takara har da Patience Jonathan


– Gwamna Rochas Okorocha yana cikin wannan jerin





Wata Kungiya ta Inyamamuran Duniya ta zabi ‘Yan takaran ta a zabe mai zuwa. An yi wannan jawabi ne bayan wani taro a Garin Enugu kwanan nan. Inyamuarai sun tabbatar da cewa babu gudu ba ja da baya a zaben shekarar 2019.

Yan Kudancin Najeriya sun fito da ‘Yan takara kusan 15 a zabe mai zuwa daga ciki akwai matar tsohon shugaban kasa watau Patience Jonathan. Inyamurai dai sun ce zabe mai zuwa ba abin da zai hana su harin kujerar Shugaban kasa. 

Sauran dai wadanda ake sa rai su dare kujerar shugaban kasar sun hada da tsofaffin Gwmanoni Orji Uzor Kalu, Peter Obi, da Gwamna Rochas Okorocha, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu da dai sauran su.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...