Yau
Dan wasan Duniya Messi zai zama Ango
- Yau Juma’a ne
auren Dan wasan Barcelona Lionel Messi
- Tuni har Jama’a sun fara cika
kauyen Dan wasan a Argentina
- Messi ya
gayyaci tsohon Dan wasan Real Madrid Di-Maria
A yau ne babban Dan wasan Duniya Messi zai shiga
daga ciki. Lionel Messi zai auri sahibar sa mai suna Antonella
Rocuzzo. Tauraron Dan Messi ya dade tare da wannan Budurwar
ta sa tun su na kananan yara.
A yau ne Dan wasa Lionel Messi na Barcelona zai zama
Ango a Birnin Rosario da ke Kasar Argentina. Dan wasa Lionel Messi zai auri Budurwar
sa da su kayi shekara da shekaru tare tun su na kanana Antonella Roccuzzo.
Tuni dai har Birnin Rosario ya cika makil wurin
daurin auren da ba a taba yin irin sa ba cikin shekaru. Abokan wasan ‘Dan
kwallon na Barcelona da sauran su sun fara hallara a jirgi. Messi ya gayyaci
‘Dan kasar sa kuma tsohon Dan wasan Real Madrid Angel Di-Maria.
Haka kuma kun ji cewa babban Dan wasan nan na Real
Madrid Cristiano Ronaldo ya samu jarirai tagwaye masu suna Mateo da Eve.
[NAIJ Hausa]