Sunday, August 13, 2017

Kalmomi 5 da Hausawa su ka aro daga Larabawa



Kalmomin Larabci da aka aro a harshen Hausa


  • Hausawa sun ari wasu kalmomi daga harshen Larabci
  • Daga cikin irin wannan kalmomi akwai sukari da Aljani
  • Ko me ya hada Malam Bahaushe haka da Balarabe?





Ba shakka Malam Bahaushe ya ari wasu kalmomin sa daga harshen Larabci. Da yawa dai daga ji za ka fahimci daga inda aka kalo su. Ga dai wasu 5 nan daga ciki yau da mu ka kawo:

  1. Sukari
Da Larabci ana cewa As-sukar wanda kuma shi ne Bature ya ke kira Sugar. Ko daga wajen wa aka fara aro kalmar?

  1. Kofi
Bature ma dai ya kan kira Kofi da suna CUP watau abin da Balarabe yake kira KAUB. Ka kuma dai ji wani sabo!

  1. Al-Jinn
Shi Bahaushe kamar Balarabe ya san da Aljannu abin da Larabawa ke kira Al-jinn. Turawa ma dai yana su kan kira su Jinns da Ingilishi.

  1. Albasa
Kusan a yare da dama Albasa ba ta canza suna ba a Najeriya. Haka dama aka san wannan suna wajen Balarabe watau Al-baslun.

  1. Sabulu

Sabulu ma dai da Larabci asalin sunan sa Sabun. Bayan wannan dai akwai aron kalmomi da dama tsakanin Hausa sa Larabci. 


[NAIJ Hausa]

6 comments:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...