Babban Dan wasan Ingila ya ajiye kwallo a gida
- Wayne Rooney yayi sallama da
takawa kasar sa leda
- Dan kwallon yace lokacin yayi da
zai bar wa yara fage
- Kyaftin din Ingila mai shekaru 31
da ya ajiye kambu
Dan
wasan gaban nan Wayne Rooney yayi sallama da takawa kasar sa leda dazu nan. Dan
wasa Rooney yayi ritaya yana shekara 31.
Babban
Dan kwallon yace lokaci yayi da zai bar wa yara fage bayan yayi shekara 14
yana bugawa Kasar Ingila wasa. Kyaftin din na Ingila mai shekaru 31 dai ya
ajiye kambu bayan tattaunawa da Kocin kasar Ingilar da kuma Kocin Kungiyar
Everton.
A
kakar bana ne dai tsohon Dan wasan nan Manchester United ya koma Kungiyar sa ta
gida watau Everton inda yanzu har ya jefa kwallaye biyu. Dan wasan yace ba abu
ne mai sauki barin Kulob din ba kuma yanzu ya ajiye kwallo a Kasar sa don ya
maida hankali da kyau.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment