Barayin kasar nan su ka sa Shugaba Buhari rashin lafiya
- Irin satar da aka yi a
Gwamnatocin baya dai ya wuce tunanin mutum
- Sowore yace barayin kasar nan su ka sa Shugaba Buhari rashin lafiya
- Mai Jaridar Sahara Reporters yace kudin da aka sata ya rikitar da Buhari
- Irin satar da aka yi a Gwamnatocin baya dai ya wuce tunanin mutum
- Sowore yace barayin kasar nan su ka sa Shugaba Buhari rashin lafiya
- Mai Jaridar Sahara Reporters yace kudin da aka sata ya rikitar da Buhari
Omoyele
Sowore yace irin mahaukaciyar satar da aka rika tafkawa a Najeriya ya sa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kwanta rashin lafiya.
Mai
Jaridar nan ta Sahara Reporters Mr. Omoyele Sowore ya bayyana wannan ne a wani taro
da aka yi a Landan. Sowore yace yanzu haka ma an gama sace kudin Kasar don haka
babu sauran satar da ake yi.
A
wani taro da aka yi a Kent a karshen makon nan Sowore yace Shugaban kasar
Muhammadu Buhari ya kwanta ne lokacin da ya fahimci irin satar da aka buga a
Najeriya. Yanzu dai Shugaban kasar ya fara murmurewa.
Yanzu
dai har Najeriya ta fita daga jerin kasashen da su ka yi kaurin suna wajen
harkar cin hanci da rashawa a Duniya. Sowore yace dole Kasashen Duniya su
taimaka wajen daina boye kudin sata daga Najeriya.
Wannan magana ta zo daidai da abin da wani Shehin Malami da aka yi a kasar ya fada a baya. Marigayi Albani yace idan har Buhari ya karbi mulki bakin cikin satar da aka yi kawai ya isa ya kwanar da shi kamar yadda 'Yaradua yayi fama da kudin wutar lantarki.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment