Ina hukuncin zuwa sallar Juma'a a
ranar Sallah?
- Mun tattaro maganar Malamai game
da faduwar idi a ranar Juma'a
- Wasu na ganin idan hakan ta faru
babu wajibcin zuwa Sallar Juma'a
- Har wasu manyan Malaman ma na
ganin cewa Sallar Azahar ta fadi
A
daidai lokacin da ake shirin bikin babban idi mun tattaro maganar Malamai game
da faduwar idi a ranar Juma'a kamar yadda za ta kama wanna karo daga wani
darasi na babban Malamin musulunci Sheikh Muhammad Sani Rijiyar Lemu.
- Magana ta farko
Malaman
Malikiyyah sun tafi a kan cewa dole ne ayi sallar Juma'a ko da ta fadi a ranar
idi don haka Allah Madaukaki yayi umarni a Qurani asali.
- Magana ta biyu
Malaman
Shafiiyah na ganin idan hakan ta faru babu wajibcin zuwa Sallar Juma'a ga
wadanda su ka fito daga kauyukan nesa amma mutanen gari za su yi Juma'a.
- Magana ta uku
Akwai
'yan mazhabar Hanabila da su ka tafi akan cewa idan hakan ta faru to sallar idi
ta dauke Sallar Juma'a.
- Magana ta hudu
Akwai
Malamai irin su Imam Shawkani da ke ganin idan Idi ya fado a Juma'a to har
sallar Azahar ta fadi amma wannan magana na sa rauni.
Magana
mafi inganci inji manyan Malamai irin su Ibn Taymiyyah ita ce za a yi sallar idi sannan kuma mustahabbi
ne Liman yayi sallar Juma'a ga masu niyya amma ba dole bane don kuwa wata idin
ta dauke wata.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment