Babban Faston Ingila ya ziyarci Buhari yace ya ga ikon Allah
-
Babban Limamin Landan ya kai wa Shugaba Buhari
ziyara
-
Faston yace ya ji dadin yadda ya ga Muhammadu Buhari
-
Justin Welby yace
warakar da Shugaban ya samu ikon Allah ne
Mai magana da yawun-bakin Shugaban kasar Najeriya
watau Femi Adesina ya bayyana cewa dazu Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wani
babban bako.
Babban Faston Kasar
Birtaniya Archbishop na Canterbury Justin Welby wanda Aminin Shugaban kasar ne
ya taka domin ziyarar Shugaba Buhari. Ba wannan bane karon farko da Limamin ya
ziyarci Shugaba Buhari a Landan.
Faston yayi murna da
yadda ya ga Shugaban kasar. Welby yace Shugaba Buhari yana samun sauki matuka
don tuni har ya murmure sosai. Babban Limamin yace wannan duk ikon Ubangiji ne
don shi ke ba da lafiya da waraka.
Dazu mu ka ji cewa Limamin Kalaba za su cigaba da yi
wa Shugaba Muhammadu Buhari addua. Shugaban
kasa Muhammadu Buhari na ta faman jinya a Landan ya kuma ji dadin wannan Fasto
Aminin sa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment