UEFA ta zabi Ronaldo a matsayin
babban Dan wasan Turai
- Dan wasan Real Madrid Cristiano
Ronaldo ne gwarzon UEFA a bana
- Yanzu nan UEFA ta zabi Ronaldo a
matsayin babban Dan wasan Turai
- Sauran 'Yan Real Madrid din sun
ciri tuta a wajen fitar da gwani da ake yi
Labari
ya iso mana yanzu nan cewa UEFA ta zabi Cristiano Ronaldo a matsayin babban Dan
wasan Turai na shekarar nan.
Babban
Dan wasan na Real Madrid Cristiano Ronaldo ne gwarzon UEFA mai kula da kwallon
kafan Turai a shekarar nan ta bana. Dan wasan ne kuma aka zaba gwarzon Dan
wasan gaba na wannan shekarar. Fitaccen Dan kwallon Ronaldo dai ya tashi da kyaututtuka
yau dinnan.
Har
wa yau sauran 'Yan wasan Real Madrid din irin su Sergio Ramos sun ciri tuta. An
zabi Ramos a matsayin Dan bayan da tauraruwar sa ta ke haskawa bana. An kuma
zabi Luka Modric a matsayin gwarzon Dan wasan tsakiya na shekarar nan ta 2016.
Dan
wasan gaban na Real Madrid ya lashe Gasar UEFA Champions league da UEFA
SuperCup na bana da bara da Kungiyar sa ta Real Madrid ya kuma jefa kwallayen
da su ka fi na kowa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment