Thursday, August 24, 2017

Wani mutumi ya tikawa Matar sa saki ta WhatsApp


An fara sakin aure ta sakon WhatsApp  


  • Yanzu cigaba fa ya kai inda ya kai a Duniyar sadarwa
  • Wannan ya sa yanzu har aure kan mutu ta kafafen zamani
  • Mutumin ya jibgawa Matar saki bayan tayi banza da shi





Mun samu labari cewa wani mutumi ya saki matar sa ta kafar sadarwa na zamanin nan na WhatsApp. Cigaba dai ta kai ana sanin idan an karanta sako a WhatsApp.

Wani Balarabe ne dai ya dankarawa Matar sa saki har 3 ta WhatsApp din a kan kurum yayi wa matar ta sa magana amma ba ta ba sa amsa ba. Abin da ya bata masa rai shi ne ta karanta sakon na sa amma tayi bakam ta kyale shi kamar ba ayi komai ba.

Yanzu cigaba ya kai inda ya kai a Duniyar sadarwa inda a kan nemi aure har ma a rabu a kafafen zamani. Sai dai akwai ta cewa wajen sakin na sa ganin ya rubutawa matar cewa ya sake ta har sau uku. Wasu dai na ganin cewa saki uku a lokaci daya ya sabawa Addinin Musulunci.


Mun samu wannan labari ne daga shafin Life in Saudi

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...