Friday, August 11, 2017

An sa mata suna 'Kuri'a' bayan an haife ta a layin zabe



An radawa wata yarinya suna 'Kuri'a' bayan an haife ta a layin zabe 

  • An haifi wata yarinya yayin da ake shirin kada kuri'a
  • Wannan abu ya faru ne a can kasar Kenya
  • An radawa wanan yarinya da aka haifa suna 'Kura'





A can kasar Kenya da ake shirin zabe an haifi wata yarinya bayan wata mata ta buge da nakuta ana shirin kada kuri'a.

Wata mata mai suna Pauline Chemanang ta buge da nakuda yayin da ake kokarin zabe a Kasar Kenya. Nan take wannan mata ta haifi diya mace a filin kada kuri'a da ke wata Makarantar Sakandare mai suna Konyaq a Yammacin Garin Pokot.


Madam Paulina Chemanang ta sauka lafiya bayan nan kuma ta dawo domin kada kuri'ar ta. Ko da aka tambayi sunan diya sai tace sunan yarinya 'kura' Chepkura. A yaren kasar Kenya na Swahili ma'anar sunan shi ne kuri'a ko kuma ka ce 'zabe'. 




[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...