Kowane
Dan Majalisar Najeriya ya karbi albashin sama da Miliyan 200
- 'Yan Majalisar sun karbi albashin sama da Miliyan 200
- A kowace wata dai su kan tashi da Naira Miliyan 10
- 'Yan Majalisar kasar dai sun ci fiye da rabin wa'adin su
Kamar yadda ku ka ji
'Yan Majalisar Najeriya sun karbi albashin sama da Miliyan 200 cikin shekaru
biyun da su ka wuce zuwa yau.
Lissafi ya nuna cewa
kusan watanni 22 ne dai kacal su ka ragewa 'Yan Majalisar kasar su sauka daga
mulki. Kowane Dan Majalisar ya kan samu kudin aiki na kusan Naira Miliyan 8 sannan
kuma ga wasu 'yan kari na kusan Miliyan guda a wata.
Tun da a wata kowane na
tashi da sama da Miliyan 8 kenan cikin fiye da shekaru biyu kowa ya karbi
akalla Naira Miliyan 214. An dai kashe fiye da Naira Biliyan 32 wajen albashin
'Yan Majalisan Kasar daga 2015 zuwa yanzu.
Jaridar Daily Trust
tayi wannan nazari inda tace dai kusan kusan rabin 'Yan Majalisa ne su ka
gabatar da kudiri tun hawan su Gwamnati yayin da sauran 'Yan Majalisa musamma na Arewa fiye da
160 kenan dai ba su gabatar da wani kudiri ba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment