Cristiano Ronaldo ya nuna cewa yana son ya dawo Ingila
- Ana ta gabza shari'a tsakanin
Cristaino Ronaldo da Hukuma
- Dan wasan ya fadawa Alkali cewa bai
aikata ba daidai ba
- Cristiano Ronaldo yace don sunan
sa ake tukhumar sa
Cristiano Ronaldo ya fusata a Kotu lokacin zaman shari'a
Ana
zargin Dan wasan Duniyan nan Cristiano Ronaldo da laifin rashin biyan haraji
har kudi €14.7. Dan wasan gaban na Real Madrid ya musanya zargin.
A
zaman da aka yi karshe Dan wasan ya fadawa Alkali mai shari'a cewa ana kokarin
a bata masa suna ne don haka aka yi masa irin wannan abu. Ronaldo yace bai taba
boye dukiyar sa ya ki biyan haraji ba. Ronaldo yace dukiyar sa ba abin da za a boye bace.
Alkalin
dai ya bayyana cewa babu ruwan sa da ko shi wanene illa iyaka aikin sa yake yi
kamar yadda ya saba. Ronaldo yace bai taba samun irin wannan matsalar a Kasar
Ingila ba don haka ne ma yake son komawa can wata rana.
Makon
nan ne aka fara shiga Kotu da babban Dan wasan Real Madrid Cristaino Ronaldo
inda ake zargin sa da laifin rashin biyan haraji a Kasar Sifen.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment