Shirin yajin aiki ya kawo dar-dar a Jami'a
- Kungiyar ASUU na shirin shiga
wani dogon yajin aiki
- Da dama na Malaman sun zabi a
tafi yajin aiki ba kakkautawa
- Shirin yajin aiki ya kawo dar-dar a wajen masu karatu
Mu
na samun kishin-kishin din cewa Kungiyar ASUU ta Malaman Jami’a na shirin shiga
wani dogon yajin aiki watakila zuwa karshen makon nan.
Kamar
yadda mu ka samu labari da dama na Malaman Jami'a sun zabi a tafi yajin aikin
da sai inna ta gani saboda rashin jituwa tsakanin su da Gwamnati. Shirin yajin
aiki ya kawo dar-dar a wajen masu karatu a halin yanzu.
A
wasu Jami'o'in irin su Usman Danfodio ta Sokoto da Ahmadu Bello ta Zariya an
fara jarrabawa a halin yanzu. Wannan dai ya raba kan daliban da ke karatu. Wasu
sun ce aikin yayi masu yawa dama can hutu su ke nema, wasu kuma na maza su
gama.
Kungiyar ASUU ta Malaman Jami’a na ganin an ba ta hakkokin ta na albashi da sauran su da kuma kyale su cigaba da jan zaren kananan makarantun da ke karkashin Jami'a.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment