Neymar zai zama Dan wasan da ya fi
kowa tsada a Duniya?
- Barcelona za ta saida Tauraron Dan
wasan ta Neymar
- Kungiyar ta ba Neymar Jr. Izini
ya tattauna da PSG
- Dan wasan zai zama mafi tsada a
Duniya idan ta tabbata
Idan
komai ya yiwu Kungiyar Barcelona za ta saida Tauraron Dan wasan ta Neymar zuwa Kungiyar
PSG na Faransa kan kudin da zai girgiza Duniya.
Barcelona
ta ba Dan wasan na ta izinin ganawa da PSG dazu. Barcelona ta sha alwashin
karbar kudi har Dalar Euro Miliyan €222. Kungiyar ta Barcelona tace dole sai an
biya wannan makudan kudi a nan take watau a zuwa daya.
Tuni
dai Dan wasan da Dillalin sa Mahaifin sa ya fadawa abokan sa cewa ya tafi kenan. Dan wasan yayi ban kwana
da abokan sa da sauran 'Yan kulob cewa zai koma Birnin Faris. Wannan dai zama
ciniki mafi tsada a Duniyar kwallon kafa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment