Tuesday, August 8, 2017

Real Madrid za ta goge raini da Manchester United


Gasar UEFA Super Cup: Man United za ta gwabza da Real Madrid

 


Kungiyar Manchester United za ta gwabza da Real Madrid

Za a kara ne a wasan cin kofin UEFA Super Cup a daren yau

Dan wasa Cristiano Ronaldo zai hadu da tsohon Kulob din sa




A daren yau Manchester United za ta gwabza da Real Madrid a filin Philip II Arena da ke Skopje a Kasar Macedonia.

Za a kara ne a kofin UEFA Super na Zakarun Turai wadanda su ka kashe kofin Champions League da Europa League a kakar bara. A cikin kwanakin nan Real Madrid ta buga da Manchester United inda kamar sauran wasannin ta ta sha kashi.

Sai dai a yau Talata manyan 'Yan wasan Real Madrid din za su dawo. Babban Dan wasa Madrid kuma tsohon Dan wasan Man Utd Cristiano Ronaldo zai buga wasan. Haka kuma kyaftin din Real Madrid Sergio Ramos. Madrid ta lashe kafin a bara.

Ba shakka dai Kocin Manchester Jose Mourinho ya san irin illar da Real Madrid za ta iya amma dai shi ma ya kawo sababbin 'Yan wasa irin su Romelu Lukaku. Haduwar Kungiyar na karshe dai Real Madrid din Mourinho tayi nasara kan Koci Ferguson lokacin yana United.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...