Ashe Bature ya kan aro kalma daga
Hausa ko Ibo?
- Akwai wasu kalmomin da Turawa su
ka aro daga Najeriya
- Turawa sun ari wasu kalmomi daga
Ibo da Hausa da Efik
- Daga cikin wadannan kalmomi dai
akwai irin su Juju da sauran su
Kamar
kwanakin baya wannan karo mun kawo maku jerin wasu kalmomi da aka aro daga
harsunan Najeriya zuwa Ingilishi. Kadan
daga ciki:
- Okra
Asali
wannan kalma ta Okra gggdaga harshen Ibo aka dauko ta. Turawa na kiran kubewa da Okra a
Ingilishi.
- Bogus
Asali
wannan kalma daga Hausa ta fito kamar yadda masana su ka fada. Yanzu Bature kan
yi amfani da wannan kalma.
- Juju
Asali
ma dai Juju kalmar daga Najeriya aka dauko ta. Juju na nufin abin da ya shafi
Aljanu ko kuma wata rawa ta mutanen mu.
- Tango
Haka
dai kalmar Tango asali daga harshen Ibibio na mutanen Kasar Kudu ta fito wanda
ainihi rawa ne na mutanen Yankin.
- Buckra
A
yaren mutanen Efik, Buckra na nufin Bawa wanda Turawa su ka ara su ke kiran
bakin mutum ko kuma Talaka farin fata.
No comments:
Post a Comment