Shin ka san yawan motocin hayan da
ke Najeriya
- Ko ka san motoci nawa ne a faadin Najeriya
- Najeriya na shan kusan lita miliyan 40 na fetur
A
yanzu haka akwai motoci kimanin Miliyan 11.5 a faadin Kasar nan. Mutanen
Najeriya dai sun kai akalla mutane Miliyan 180. Hakan na nuna cewa a cikin
mutum 15 akalla a samu mutu guda mai
mota.
Kashi
58.5% cikin motocin da ake da su a Najeriya na haya ne watau wadanda ake amfani
da su wajen kasuwanci. Wadannan motoci ne su kafi kowane yawan hadari da kuma
rasa ran Jama’a bisa titunan Najeriya.
Kashi
40.2% kuma na motocin da ake da su na jama'a ne watau na-kan su. Ana da motoci
sama da Miliyan 4.5 wadanda su ke ba na haya ba. Akwai kuma wasu motocin na
Jami'an Gwamnati da sauran Kungiyoyin kasa-da-kasa na kimanin kashi 1.4%
wadanda wasu a kan mara masu baya.
Mun samu wannan alkaluma ne daga bakin Shugaban
Hukumar tara alkaluman kasa watau Hukumar NBS Dr. Yemi Kale.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment