Friday, August 11, 2017

Za a hau yanar gizo kyauta yau a Najeriya


Albishirin ku: Masu layin GLO za su ci bagas


 
  • Globacom za su bada goron Juma'a a Yau
  • Masu layin za su hau yanar gizo a kyauta
  • Sai dai akwai wasu sharuda kafin a dace



Labari ya zo mana cewa masu layin Glo za su gwangwaje kyauta yau a Najeriya muddin sun sa katin waya ciki 'yan kwanakin nan.

Kamfanin sadarwa na Globacom na kasar za su bada goron Juma'a  wanda shi ne karo na farko a Kasar domin a hau shafin gizo kyauta ba tare da ko sisi ba. Za dai a bada kyautar mega byte 200 domin a yi abin da aka ga dama.

Kenan dai masu layin za su hau yanar gizo a kyauta goben. Sai dai akwai wasu sharuda kafin a dace da wannan wanda shine mutum ya zama yayi amfani da katin waya na N250 ko kuma ya kashe mega byte na hawa yanar gizo 100 da kuma N150.

Kwanaki dai Hukumar NCC da ke kula da harkokin sadarwa na zamani tayi kira ga jama'a da su saurari sabon farashin hawa shafin Internet. Mun kuma ji kishin-kishin din ana kokari a dakatar da wannan bagas da GLO za ta bada.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...