Wednesday, August 16, 2017

UEFA ta fito da gwarzon 'Yan kwallon shekarar nan


Manyan ‘Yan kwallo 3 da za a zaba zakaran Turai


An kawo Ronaldo cikin manyan 'Yan wasan Turai

Haka kuma an sa takwaran sa Lionel Messi na Barcelona

Na karshen su shine Dan wasa mai tsaron raga Buffon




A jiya UEFA ta fito da gwarzon 'Yan kwallon shekarar nan guda 3 wanda a cikin su ne za a fitar da gwani na gwanaye. Kun dai ji 'Yan kwallon su ne:

  1. Cristiano Ronaldo
Dan wasan gaban na Real Madrid ya lashe Gasar bana na UEFA Champions league da Kungiyar sa ta Real Madrid ya kuma jefa kwallaye a wasanni karshe da na kusa da karshen da su ka kawo nasara.

  1. Lionel Messi
Duk da Dan wasan bai isa zagayen karshe na Gasar UEFA Champions league ba amma yana cikin wadanda su ka yi zarra kamar kowace kaka a Turai. Messi ya jefa kwallaye rututu a Gasar bara.

  1. Gianligui Buffon
Dan wasan da ke tsaron ragar Juventus ya samu shiga bayan irin kokarin da ya tabuka a bara. Kafin wasan karshe dai kwallaye kadan aka iya zurawa Buffon a ragar sa.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...