Neymar zai rika karbar albashin Biliyoyi a shekara
Yanzu Dan wasa Neymar zai rika karbar albashin Biliyoyi a shekara
A kowace rana ta Allah zai tashi da sama da Naira Miliyan 30
A kowace awa guda Dan wasan zai samu sama da Miliyan guda
Ko barci Neymar yayi ya
tashi a rana ba mamaki zuwa wannan lokaci ya hada kusan Naira Miliyan 10 a
sabon Kulob din da ya koma PSG.
Dan wasan da a cikin
talauci ya tashi ya amince da yarjejeniyar shekaru biyar inda za a kashe kudi
har sama da Dala Miliyan 500. A kowace rana ta Allah Neymar zai tashi da akalla
Naira Miliyan 36.
Da mu kayi lissafi dai
mun fahimci cewa Dan wasa Neymar zai rika karbar albashin sama da Naira Biliyan
uku a shekara. A kowace awa guda Dan wasan zai samu sama da Miliyan guda na
Naira.
Dama dai kun ji cewa Idan komai ya yiwu Kungiyar Barcelona za ta saida
Tauraron Dan wasan ta Neymar zuwa Kungiyar PSG na Faransa kan kudin da zai girgiza
Duniya.
[NAIJ HAUSA]
No comments:
Post a Comment