Abin alfahari: Dan Najeriya
ya zama ‘Dan damben Duniya
– Wani asalin dan Najeriya ya doke Klitschko a wasan dambe
– Yanzu haka ya karbi kambun damben
Duniya
– Wladmir Klitschko ya sha kashi hannun Joshua
A
wani wasan damben Duniya da aka yi a Kasar Ingila wani ainihin Dan Najeriya ne
yayi nasara. Wannan dai abin farin ciki ne ga ‘Yan kasar da kuma daukacin
bakaken Mutanen Afrika baki daya.
Anthony
Joshua ya gabje Wladmir Klitschko a damben Duniyar da aka gwabza a filin wasa
na Wembley da ke Birnin Landan inda mutane kusan 90, 000 su ka hallara gudun a
gani a ba su labari.
Yanzu
haka Joshua wanda asalin sa Dan kasar Najeriya ne ya karbe kanbun damben
Duniyar na Heavyweight inda ya zama
zakara bayan ya tika Zakaran Duniya Wladmir Klitschko da kasa a kusan zagaye na
daf da karshe.
Anthony Joshua ya bayyana sirrin karfin da yake da shi yace ba zai rasa nasaba da sakwara da teba da sauran abincin 'Yan Najeriya ba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment