Kocin Man Utd Jose Mourinho ya dauki fansa
– Man
Utd ta ba Chelsea kashi a Gasar Firimiya
– Kungiyar Manchester ta ba doke
Chelsea da ci 2-0
– Chelsea sune a kan saman teburin
Gasar
A bangaren wasanni cewa Kungiyar
Manchester United ta ba Chelsea kashi a Gasar Firimiya ta Ingila. Man Utd din
dai ta doke Chelsea ne da ci 2 da nema ta hannun Dan wasa Rashford da kuma
Ander Herrera.
Chelsea
ce dai ke saman teburin Gasar na Firimiya amma kuma hakan ya sa ta rage maki
inda Tottenham ke jiran ko-ta-kwana. Kocin Chelsea Conte yace sun yi sakaci a
wasan kuma ya dauki laifi.
A
farkon kakar bana dai Chelsea ta dagargaza Man Utd a Filin Stamford Bridge da
ci 4-0. Wannan karo tsohon Kocin Chelsea Jose Mourinho ya dauki fansa. Tun da
Koci Mourinho yake wasa a Ingila dai babu kulob din da ta taba dukan sa
gida-da-waje.
Barcelona
da Real Madrid sun yi nasara a Kasar Spain da ci 3-2 inda Isco da Lionel Messi
suka jefawa Kungiyar su kwallaye biyu. A kasar Italiya kuma kunnen doki aka yi
tsakanin Inter Milan da AC Milan.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment