Gwamnatin Jihar Kano ta damke
mabarata da dama
– Gwamnatin Jihar Kano ta kama masu bara fiye da 400 a Jihar
– Hukumar Hisbah ce dai tayi wannan aiki a
fadin Jihar
– Dama Sarki Muhammadu Sanusi II yace Arewacin
Najeriya sun fi ko ina talauci
Hukumar
Hisbah ta Jihar Kano ta kama masu bara da roko a Jihar Kano da dama cikin watan
jiya da shekaran jiya kamar yadda mu ke samun labari yanzu haka. An dai
kafa dokar da ta haramta bara a cikin Garin Kano.
Shugaban
Hukumar Hisbah Malam Musa Tsangaya ya bayyanawa manema labarai wannan kwanan nan. Tsangaya yace an kama masu bara a
cikin Jihar wanda ya saba doka. Cikin dai wanda aka kama akwai manyan mutane
kusan 200 yayin da sauran kuma dai kananan yara ne.
Mafi
yawan wadanda aka kama dai ‘Yan asalin Jihar Kano ne yayin da sauran kuma su ka
fito daga Jihohin Kaduna da Jigawa masu makwabtaka da Kano. Cikin wadanda aka
kama dai har da maras hankali.
Kwanan
nan Sarkin Kano ya bayyana cewa Arewacin Najeriya sun fi ko ina talauci a wani
taro da aka yi a Kaduna. Akwai Almajirai sama da miliyan 3 a Jihar Kano kurum.
This comment has been removed by the author.
ReplyDelete