Saturday, April 29, 2017

HUDUBAR JUMA’A DAGA ITN-ZARIA



HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA


Watan Sha’aban; Jakadan Ramadan-Daga Bakin Imam Sheikh S. S Abubakar






A’udhu BilLahi minas Shaidan Ar-Rajim,
BismilLahir Rahman Ar-Raheem,

Godiya sun tabbata ga Allah, muna yabo gare sa Madaukakin Sarki. Muna shaidawa lallai babu abin bauta da gaskiya face Allah shi kadai ya ke wanda ya shar’anta ga Bayin sa tafarkin da zai kai ga samun yardar Sa. Muna shaidawa lallai Shugaban mu; Annabi Muhammad SAW Bawan Allah ne kuma Manzon Sa, wanda ya shiryar da Al’ummar sa ga yin biyayya ga sunnar sa.

Bayan haka:
‘Yan uwa a yau muna cikin rana ta farko na Watan Sha’aban wanda Manzon Allah SAW ya kasance yana damuwa da shi saboda abin da aka ruwaito daga Usama Dan Zaid RA, yace: Na ce da Manzon Allah SAW meyasa yake azumi a cikin Watanni amma ba kamar yadda yake yin azumi a Watan Sha’aban ba? Sai Manzo SAW yace: Saboda wannan wata ne da Mutane su ke rafkana da shi wanda yake tsakanin Rajab da kuma Ramadan kuma wata ne wanda a cikin sa ana daukaka ayyuka zuwa ga Allah, sannan Ni ina so a daukaka ayyuka na ina mai azumi. Imam Al-Nisa’i ya ruwaito wannan Hadisi kuma Malaman Hadisi sun inganta shi.

Kenan Annabi SAW yana son Azumi a cikin wannan wata saboda a cikin sa ake daukaka aiki a gaban Allah Madaukaki inda yake so a bayyana ayyukan sa yana mai azumi. Wannan wata dai shi ne Jakadan mai martaba wanda yake zuwa kafin abin so mai girma da daraja. Shi dai wannan wata Sha’aban shi ne Jakada na watan Ramadan abin son mu. Kuma wannan zai kasance ne ta hanyar aikata al’amura masu sauki ga wanda shi damuwar sa ya samu yalwa da haske a cikin kabarin sa bayan mutuwa. Kuma abubuwa ne da Mutum zai gabatar idan har manufar sa ya samu jin kai da yardar Ubangiji SWT, wanda ya kasance haka ne tunanin sa zai yi kokari ya girmama Jakada ga watan Ramadan.

Ta yaya ake girmama wannan Watan? Ta yin Azumi a cikin sa kamar yadda Hadisi ya gabata da kuma abin da aka ruwaito daga Aisha RA inda ta ke cewa: Ni, ban ga Annabi SAW yana cika Azumi wani Wata in ba Ramadan ba, amma kuma ban taba ganin Watan da yake yawaita Azumi ba kamar Watar Sha’aban. A wata ruwayar Nana A’isha RA ta ke cewa Manzo SAW yana azumtar daukacin Watan. Don haka ya kamata muyi kwaikwayo da wannan Sunnah na yawaita Azumi domin karrama wannan Wata.

Abu na biyu da za muyi domin karrama wannan Watan da yake Jakada na Ramadan shi ne mu tsarkake rayuwakan mu daga abubuwa na zunubi da kuma sabon Allah. Gidajen mu su tsabtatu daga duk wata kazanta. Sannan kuma a kula da tuba Bayin Allah; tuba ta nasiha zuwa ga Allah. Mu kuma yi kokari mu ga abin da zai zama sulhu tsakanin mu da Mahallicin mu; mu bude wani sabon farin shafi ga abin da yayi saura na rayuwar mu kuma kullum mu rika jin albishir da cewa Allah zai yafe mana idan mu ka nemi ya yafe kana ya karbi tuba ba tare da cire tsammani ba,  kamar yadda aka fada a Al-Kur’ani cewa ka da a yanke tsammani daga gafarar Ubangiji don lallai Allah yana yafe zunubai baki daya domin shi mai yawan gafara ne da jin kai.

Saboda haka ‘Yan uwa Musulmi sai duk mu yawaita kwadayi na cewa ka da Watan Ramadan ya shigo mana face cewa muna cikin tsarki da tsabta a wannan Wata da za muyi tattali. Sai mu kiyayi wani abu na shirka wanda Allah SWT yayi alkawari ba zai yafewa duk wanda ya mutu yana kai ba. Shirka dai abu ne da ya zama ruwan dare a yau, Jama’a na rayuwa cikin Mutane da yawa ba tare da sanin haka ba. Dole ne ayi kokarin kaucewa Shirka. Mu’amular da Jama’a ke yi na jefa su hannuwan Bokaye masu yi masu alkawari na banza su na nuna masu cewa za su yi masu abubuwan da babu mai yin su sai Allah Sarki. Haka kuma ga Shirka ta riya da ta ke bayyana wanda Mutum ba zai aikata alheri ba sai dai don a gani a yaba. Wannan duk ya kamata mu kaurace masu.

Sannan kuma mu kiyayi zalunci duk irin zalunci da Shari’a ta fada don ba shi da rana. Kamar yadda ba za mu so a zalunci namu ba, don Allah ya fada da kan sa cewa shi ya haramtawa kan sa zalunci, don haka mu ma ka da mu yi zalunci mu nisance sa kamar yadda Shari’a ta fada. Sannan kuma ya kai wanda hakkokan Mutane ya ke gare ka, ka tabbatar cewa ka da ka tare hakkin wani ko har wani yayi kuka da kai. Wannan yana cikin aikin zalunci wanda bai dace duk wani mai jiran Rahamar Allah SWT yayi ba.

Ya kai wanda ka ke kangarewa ga Mahaifan ka, ya kamata ka nemi yardar Allah SWT ta kofofin da ake samun yarda. Daga cikin wadannan kofofi akwai hanyar biyayya ga Iyaye. Saboda haka idan kana da iyaye kuma har Allah ya hada ka zama da su. Ka yi kokari ka samu yardar su don biyayya gare su wajibi ne idan har bai saba fushin Allah ba. Fushin Allah kuma yana ga fushin Mahaifa idan har sun yi bisa ga abin da su ke da hakki a kai.

Girmamawa na uku da za muyi wa wancan Wata shi ne mu yawaita karatun Al-Kur’ani. Hakika wadanda su ke magabata kuma managarta shugannin mu su na iya bakin kokari na tattali domin shiga cikin Watan Ramadan. Ga duk wanda ya san irin falalar Watan Ramadan ba zai yarda cewa sai ta shigo kafin ya fara azumi ba watau tattalin abin cin riba na Watan. Wanda yake Dan kasuwa mai hangen nesa zai yi tattali ne tun kafin Ranar kasuwa ya ci riba, ba sai Ranar ne zai nemi kayan da zai sayo sannan ya saida ba. Don haka dai komai yana bukatar shiri; Magabatan mu kan yi shirin ne domin cin ribar Watan Ramadan. Ba su kyale Duniya ta rude su har su shantake ba wanda Duniya mai yawan yaudara ce da makirci da rudurwa. Saboda haka ya kai wanda ka ke so ka mori Watan Ramadan ta ya za ka samu ganima na wannan Wata sai ka takar-kare ka dage da ayyuka. Ta ya za ayi wannan ba tare da tsarkake dukiya ba ko wanda yake cikin tabon shan kayan maye da aikata ashha na zunubai? Ta ya Mutum zai ji dadin karatun Al-Kur’ani a watan Ramadan alhali bai tsarkake harshen sa daga giba ba ko kuma cin dukiyar Jama’a ba? Annamimi, ko ta ya zai amfana da Watan Ramadan idan har yana wannan dabi’a? Ta ya Mutumin da zuciyar sa ke cike da keta da kiyayya da hassada ga Musulmai zai yi tsammanin amfana da wani abu na Watan Ramadan? Ta ya ya Mutum da yake kasance tsundum cikin abinci da suturar Haramun zai samu Allah SWT ya amsa masa addu’ar sa kamar yadda Imam Muslim ya ruwaito.

A sani Bayin Allah cewa Ubangiji Allah SWT Tsarkakakke ne wanda bai karba face tsarkakakke, mu yi kokari wajen rabuwa da duk wani mugun hali ko dabi’a, mu tsarkaka wajen duk abin da Allah SWT ba ya so a ko ina. Lallai Allah SWT ya umarci masu imani da irin abin ya umarci Manzonin sa na cewa: Ku ci daga abu mai tsarki ku kuma yi aiki na gari. Wannan kuma shi ne umarnin da ke kan sauran masu imani. Ka da Mutum dai ya zama ya ci face daga mai tsarki ta kowace fuska.



Allah ya ba mu fahimtar Al-Kur’ani mai girma, ya amfane ni da ku duka daga ayoyi masu wa’azi na hikima. Allah ya tsare ni da ku daga azabar wuta mai radadi don kuwa shi mai ji ne kuma mai gani. Allah ka dada tsira da Annabi Muhammmad SAW da Iyalin sa ka tabbatar da yardar ka da Sahaban sa ka kuma buwayar da Addinin Musulunci, ka rugurguza makiyan mu. Allah ka cika ayyukan mu da abin da zai zama alheri a gare mu ka tserar da mu da kunyar Duniya da lahira.




Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter: @Ya_waliyyi





No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...