Ronaldo
ya kai Real Madrid zagaye na gaba a Gasar UCL
– Real Madrid ta kara ba Kungiyar Bayern Munich kashi
– A zagaye na biyu an tashi 4-2 a
gidan Madrid
– Cristiano Ronaldo ya kara jefa
kwallaye 3
A
bangaren wasanni Zakaru Real Madrid sun yi waje da Kungiyar Bayern Munich ta Kasar Jamus
daga Gasar UEFA Champions league na zakarun Nahiyar
Turai a wasan jiya Talata.
A wasan farko kuna da
labari cewa Real Madrid ta doke
Bayern Munich da ci 1-2 a gasar. Haka wannan karo Real
Madrid ta kara ba Kungiyar Bayern Munich kashi a wasan zagaye
na biyu inda aka tashi 4-2 a gidan Santiago na Madrid.
Dan
wasan Duniya Cristiano Ronaldo ya jefa kwallaye 3 duk shi kadai a wasan inda ya
zama dan wasan farko da ya zura kwallaye 100 a Gasar UEFA Champions league. Sai
dai Jama’a sun yi korafi game da yadda Alkali ya busa wasan.
Har
wa yau Atletico Madrid ta doke Leicester City ta Ingila inda tayi waje a Gasar.
Haka kuma yau za a fafata tsakanin Juventus da Kungiyar Barcelona. Dama wancan
makon Monaco ta ba Dortmund kashi a Jamus.
No comments:
Post a Comment