HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA
Wahalar Duniya-Daga Bakin
Imam Sheikh S. S Abubakar
A’udhu BilLahi minasshaidan
Ar-Rajim,
BismilLahir Rahman
Ar-Raheem,
Dukkan godiya sun tabbata ga
Allah, wanda yake bada Duniya ga wanda yake so da wanda ma ba ya so. Amma ba ya
bada lahira face ga wanda yake so, muna yabo da godiya gare sa Madaukakin
Sarki. Muna neman tsari da hasken zatin sa mai daraja daga duk abin da zai samu
cikin aikin gajiya da wahala. Muna rokon sa ya dawwamar da mu a cikin gidan sa
na aminci inda yake babu yasasshiyar magana da kururuwa na ihu. Muna shaidawa
lallai babu abin bauta da gaskiya sai Allah shi kadai wanda gare sa komawa take.
Sannan Shugaban mu; Annabi Muhammad SAW Bawan Allah ne kuma Manzon Sa ne wanda
ya zo mana da mafi adalcin hukunce-hukunce alhali bai yi karatu ko rubutu ba.
Bayan haka:
Ku sani ‘Yan uwa an gina
rayuwar ‘Dan Adam ta Duniya bisa ga wahala da yin ayyuka masu gajiyarwa da yin
gwagwarmaya da fadi-tashi kuma babu hutu a cikin wannan rayuwa ta Duniya. Allah
Madaukakin Sarki yana cewa ya kai Dan Adam lallai kai mai wahala ne, mai
fadi-tashi a yayin da kake kokarin komawa ga Ubangijin ka.
Saboda haka ya kai ‘Dan uwa
ka sani cewa a duk wani lokaci kana ketawa ne cikin lokacin da aka diba maka na
doron kasa a yayin da kuma ka ke ketawa kana ta fadi-tashi ne a cikin rayuwar
ka. Babu mutumin da zai zauna a cikin rayuwar sa yace babu fadi-tashi sai dai
hutu, dole sai yayi fadi-tashi komai matsayin sa da dukiyar sa, illa yanayi ne
kurum yake bambanta. A ko yaushe haka za ka cigaba da wannan har ka sadu da
Ubangijin ka domin a gare sa wurin komawa ya ke.
Wannan fadi-tashi ko ya zama
ta hanyar wani aiki da za kayi da jikin ka ko kuma ta hanyar wata gwagwarmaya
na abin da za kayi da tunanin ka ko hankalin ka. Saboda haka Dan Adam ka sani
cewa ba za ka samu hutu ba har abada. Ana samun hutu ne bayan an komawa Allah
amma fa ga wanda yayi abin da za a sama masa hutun watau na gabatar da biyayya
da da’a ga Ubangiji. Mu sani ‘Yan uwa lallai duk abin da ke cikin wannan Duniya
tamkar inuwa ce wanda za ta gushe; duk wani rai da mukami da dukiya da Allah
zai ba ka aro ne na wani lokaci kafin Ubangiji mai shi ya karbe abin sa.
Annabi SAW ya siffanta Duniya
kamar kurkuku ce ta Mumuni mai imani sannan Aljanna ce ta Kafiri wanda Imamu
Muslim ya fito da wannan Hadisi. Kurkuku wuri ne mai tsanani da kunci da wahala
saboda Mumuni kullum a Duniya yana cikin fadi-tashi da gwagwarmaya na biyayya
ga Ubangijin sa da kuma sabawa abin da rai da zuciya da ma shaidan yake so.
Kullum mai imani na kokarin samun yardar Allah Ubangiji, don haka Duniya tamkar
wanda aka takurawa ne ga mai Imani. Shi kuwa kafiri Aljanna ce a wurin sa don
kuwa bai damu da ya lazumci dokokin shari’a ba, kuma ba ya shiryuwa da wani
Addini ko tafarki na gaskiya ko ya mika wuya ga Ubangiji. Shi Kafiri a kullum
bukatar sa tana kan bukatun ran sa tamkar ya samu Aljanna kenan tun da yana
abin da ya ga dama.
Ya Kai ka sani cewa duk wani
Dan Adam da yake wani kokari yana fadi-tashi ya kan hadu da abin da ba ya so a
cikin Duniya wanda wannan da Musulmi da Kafiri; Mace da Namiji; Mai kudi da
Matsiyaci duk daya su ke. Sai dai akwai bambanci; watau wani shi wahalar sa
tana ga biyayya ga Allah da Addinin sa. Akwai kuma wanda duk wahalar sa ba ta
wuce ta sha’awar sa ba. Don haka akwai bambanci tsakanin wanda yake wahala
wajen cigaban al’umma da yada manufofi na alheri da tunkude duk wani tsanani da
kunci da wanda ya damu kurum da sha’awowin da sabon Allah da jawo fushin
Ubangiji a cikin gwagwarmayar sa. Wadannan mutane su na raba kawunan Jjama’a suna
zubar da jini tare da ha’intar mutane.
Don haka dai wahala da
fadi-tashi ya zama dole, sai dai abin tambayar shi ne a kan menene mutum yake
wahala? Wannan manufar ita ce abin dubawa. Duk wanda yace ba zai kara wani aiki
na wahala ba yayi karya. Abin da ake so ya zama duk wahala da za ayi, ta zama
wahala ce mai riba. Allah yake fada mana a Al-Kur’ani cewa ko shin za mu sanya
al’amurran Musalmai wadanda su ke biyayya ga Allah da wadanda su ke keta
iyakokin Ubangiji? Allah yace ta ya ma za su zama daya??? A wani Hadisin kuma
na Imam Muslim, Annabi SAW yake cewa Al-kur’ani hujja ne a gare ka ko a kan ka.
Saboda haka kowane cikin mu
idan ya fito wahala kullum sai ya rika tambayar kan sa ko shin abubuwan da yake
yi na kirki ne ko wanda za su dulmiya sa cikin wuta. Wahalar da ake magana
watau mutum ya tafi zuwa wajen sana’ar sa, kai ko wurin hira mutum ya tafi, ya
duba ko shin me yake kokarin samu a wannan hira. A kan haka ne za a auna
kai-kawon mu a ga ko a kan me muke wahala. Wannan shi ake so mu rika tambaya
kullum ba jifa-jifa ba; mutum ya duba kan sa domin yayi farin ciki ko kuka da
nadama idan yayi daidai ko akasin haka.
Mu sani a Duniya daga
Ma’aikaci ko ‘Dan kasuwa ko wani Mai sana’a ko Mai mukami kowane dai akwai
rawar da yake takawa a cikin aikin na sa. Duk wanda yake wannan wahala domin
samun yardar Allah ko da kuwa zai samu wani abu na Duniya sai ka ga yana samun
aikin sa gwanin kyau. Irin wannan mutumi yana mai yawan hallarto Allah yana
gujewa haram kuma ba zai yarda Duniya ta rude sa ba komin yaya. Kai komai
karfin abokan gaba wannan mutumi ba zai rabu da addinin sa da ka’idojin sa ba komai
makirci da rudani ko yawaitar barna. Wannan mutumi zai yi wahala amma fa ba ta
banza ba wanda iyakar ta zuwa lokacin rayuwar Duniya don abin da Allah mai
girma ya masa tanadi shi ya fi wanzuwa.
Allah SWT yake cewa: Hakanan
muka yi wahayi watau ga Manzo Annabi na Al-kur’ani cikin larabci domin ka
gargadi mutanen Garin Makkah da sauran Mutane na Garuruwa domin yi masu kashedi
da Ranar Kiyama inda za a kasa Mutane gida biyu. Saboda haka kullum mu rika yi
wa kan mu hisabi muna duba ko wahalar mu ta banza ce domin mu ci riba a Duniya
da lahira.
Allah ka ba mu fahimtar
Addini ka tseratar da mu daga azaba mai radadi ka karbi ayyukan mu ka dada
tsira ga Annabi Muhammadu SAW da wadanda su ka bi tafarkin sa. Allah ka buyawar
da addinin ka kuma kayi maganin abokan gaba. Allah ka jikan masu rauni ka
karfafa masu ka gafarta mana akan abin da muka zame ciki. Allah ka yaye mana
musiba ka sa ayyukan mu su zama na gari. Allah ka sa kar muyi wahalar banza a
Duniya. Allah ka shiryar da shugabannin mu ka sa su aikata alheri Duniya da Lahira.
Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga
Masallacin I.T.N-Zaria.
Twitter: @Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment