Abubuwa 3 da su ka sa ‘Yan
Boko Haram su ka gagara
– Ana kan nasara wajen murkushe ‘Yan Kungiyar Boko Haram
– ‘Yan ta’addan sun kashe dinbin
mutane a Yankin kasa da Nahiyar
– Ko ya aka yi suka yi wannan karfi
haka a Duniya?
Wani
Marubuci mai suna Theophilus Abbah ya zayyano dalilan da su ka sa Boko Haram
tayi karfi. Duk
da sakacin Hukuma akwai wasu dalilai da har su ka kawo Kungiyar tun farko. Na tsakuro daga ciki:
1. Jahilci da rashin aikin yi
Boko
Haram tayi amfani da Jahilcin Matasa da kuma rashin sana’a inda aka nuna masu
cewa aikin Allah su ke yi dama can ba su da wani aikin kuma ba su san Allah ba.
Ko da wasu kadan cikin su na da karatu.
2. Makamai
Boko
Haram ta samu makudan kudi na sayen makamai da kuma makaman kan su daga wurare
da dama. Ciki dai har da ta Arewacin Nahiyar bayan da Kasar Libya ta fadi daga
hannun Marigayi Shugaba Moumar Gaddafi.
3. Kashe makiya Kafirai
Ko
da akwai rikicin siyasa tsakanin kungiyar sai dai sun yi tarayya wajen ganin
bayan Kafirai da wadanda su ke kira Dagutu. Wajen su ko da an mutu wajen wannan
gaba ta kai mutum.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment