Yadda fadar shugaban kasa tayi amai ta lashe
– Kwanaki aka kori wani Dan jarida daga fadar shugaban kasa
–
Jim kadan kuma sai ga shi an maido sa
–
Hakan ya jawo alamar tambaya a kasar
Idan kuna biye za ku san cewa a farkon makon da ta wuce shugaban masu tsare shugaban
kasa Bashir Abubakar ya kora wani Dan Jaridar Punch daga fadar shugaban kasar a
cewar yayi wani rahoto game da lafiyar shugaban kasa Buhari.
Jim kadan kuma sai ga
shi shugaban kasar ya bada umarni a maido Olalekan Adetayo ya cigaba da aikin
sa. Shugaban kasar ya bayyana cewa Bashir Abubakar bai tuntube sa kafin ya
dauki wannan mataki ba.
Shugaban kasar wanda
tsohon Soja ne dai yana cikin abin da ya fara yi hawan sa mulki dawo da wani
Dan jaridar kasar waje da aka kora a lokacin shugaba Jonathan ya cigaba da
aikin sa domin nuna riddar sa zuwa Damukaradiyya.
Olalekan Adetayo ya
bayyana cewa ana cewa ana neman sa dama dai yayi wuf ya kira mai magana da
bakin shugaban kasar Femi Adesina. Nan gaba dai maganar za ta kara fitowa don
kuwa Dan jaridar ya bayyana cewa shugaban kasar bai lafiya.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment