Abubuwan da ya kamata ka sani game da mugun cutar nan
Cutar sankarau dai ta addabi bayin Allah har wani Gwamna ya furta cewa zunuban Jama’a ne ya kawo cutar, ko da yake dai ya
lashe aman na sa. Cutar dai na taba lakar baya da kuma kwakwalwa, yanzu haka da
dama a lahira.
1.
Cutar
sankarau iri-iri ce
Kwayoyin cuta iri dabam dabam ke kawo ta. Sankarau ta kashe
sama da mutane 120,000 a Duniya
2.
Saurin
magani bai kawo lafiya
Wai don ayi gaggawar fara daukar matakin kiyaye cutar bai
nuna cewa za a samu sauki
3.
Sankarau
na iya kashe kowa
Ita sankarau tana iya kama kowa babba da yaro. Sai dai ta fi
kama kananan yara da ‘yan samari.
4.
Rigakafi
ce hanyar tsira
Neman magunguna tun kafin cutar ta buge mutum ne babbar
hanyar tserewa cutar mai kisa.
5.
Shaye-shaye
Shaye-shaye na iya sa cutar da kara yaduwa da kyau a jikin
mutum. ‘Yan sigari sai ayi hattara.
6.
Najeriya
na cikin matsala
Kasashe da har yanzu ke fama da talauci irin su Najeriya na
cikin hadari. Rashin magani da wurin kwanciya mai kyau na da babbar
illa.
7.
Daukar
cutar
Yanzu sai mutum ya kamu da cutar bai sani ba ta iska don
haka sai an kiyaye kwarai.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment