Tuesday, April 4, 2017

Boko Haram sun yi wani sabon bidiyo

Labari da Dumi-Dumi: Boko Haram su yi wani sabon bidiyo



Yanzu nan ba da dadewa ba mu ke samun labari cewa kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo wanda ta nuna shugaban kasa Muhammadu Buhari da dan yatsa. 

Bayanai na zuwa mana cewa Bangaren Abubakar Shekau na Kungiyar Boko Haram sun fitar da wani sabon bidiyo inda su ka taba shugaban kasar Muhammadu Buhari da kuma wasu manyan na Gwamnati.

A dan gajeren bidiyon an ga ana zabgawa wasu kauyawa bulala a dalilin laifuffukan da su ka aikata ba mamaki a kewayen Dajin Sambisa ne abin ya faru. An samu wadannan mutane ne da laifin shan giya da amfani da kwayoyi.

A bidiyo ‘yan ta’addan suna rike da hotunan wasu manyan shugabannin Duniya da ma shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya. Ba dai wannan bane karo na farko da Boko Haram su ka fitar da Bidiyo kwanan nan.



[NAIJ Hausa]






No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...