UEFA
Champions league: Juventus sun gagari Lionel Messi
– Barcelona tayi waje daga Gasar UEFA Champions league
– Juventus ta doke Barcelona tun a zagayen
farko
– Wannan karo an tashi 0-0 ba tare
da ci ba
An
yi waje da Kungiyar Barcelona daga daga Gasar UEFA Champions
league na zakarun Nahiyar Turai na kakar bana a jiya inda su ka fafata da
Juventus. Yanzu Juventus ta karasa zagaye na gaba.
An dai tashi wasan ne
babu ci sai dai a karo na farko Juventus sun doke Barcelona da ci 3-0. A wancan
karo Dan wasa Dybala ne yayi tashe. Wannan karo dai Barcelona sun yi kokarin
rama kwallayen amma Juventus su ka kare ragar su.
A zagayen baya Barcelona
ta fitar da PSG bayan da farko ta sha mugun kashi wannan karo dai duk da ‘Yan
wasan Barcelona abin ya faskara. Dama can Real Madrid sun yi waje da
Kungiyar Bayern Munich daga Gasar a wasan Ranar Talata.
Dortmund ta yi waje bayan
da Kungiyar Monaco ta kara lallasa ta da ci 3-1. Yanzu dai ba wata Kungiyar
Jamus da Ingila a Gasar.
[NAIJ Hausa]
I truly like you're composing style, incredible data, thankyou for posting. Barcelona Jersey Online
ReplyDelete