Wednesday, April 5, 2017

Ta jefar da jinjirin da haifa a bola


 Wata mata ta jefar da jinjirin da haifa a bola



 Kadan daga cikin aikin CCTV 

A wannan zamani da ake ciki na kimiyya da fasaha an gano yadda wata mahaifiya ta jefar da jinjirin da ta Haifa a cikin bola saboda tsabar rashin imani.

Muna da labarin yadda wata mata a can kasar Sin watau China ta jefar da jinjirin da ta haifa a cikin kwandon shara. A wannan zamani na fasaha dai tuni aka kama ta a dalilin na’urar daukar hoto na CCTV.

Wannan mata dai da ta fito daga Garin Shenzen da ke kasar China ta tashi ne takanas a Ranar Asabar ta jefa jinjirin ta da ke cikin wani akwati a cikin bolar shara. Wani mai shara ne dai ya tsinci jinjirin tsamo-tsamo cikin jini amma da ran sa.

An dai wuce da jinjirin asibiti a dalilin rauni da ya samu a daidai idanun sa nan dai aka duba sa. Daga baya kuma Jami’an ‘Yan Sanda su ka binciko wanda ya jefar da wannan jinjiri nan take su ka far ma gidan wannan mata kuma aka kama ta tsamo-tsamo.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...