‘Yan wasan Real Madrid da Barcelona sun bar tarihi
– Neymar Jr. ya ci kwallon sa ta 100 a Barcelona
– Shekarar Neymar kusan 4 a Kungiyar Barcelona
– Haka ma Real Madrid ba a bar ta a
baya ba
Dan
wasan gaban nan na Barcelona watau Neymar Jr. ya jefa kwallon san a 100 a zaman
sa a Barcelona jiya a wani wasa da su ka buga. Barcelona dsi ta lallasa
Kungiyar Granada da ci 4- 1 a wasan na
La-liga.
Hakan na nuna cewa da wuya dan wasa Neymar
ya bar Barcelona bayan da ya ci kwallon san a 100 a cikin wasanni 177 rak bayan
zuwan sa Kungiyar shekaru 4 da suka wuce. Neymar da Messi da Suarez dai sun addabi 'yan bayan Duniya
Haka
kuma Real Madrid ta lallasa takwarar ta Alaves da ci 4-0 watau har da nema.
Kusan dai Barcelona da sauran manyan Kungiyoyin kasar Spain sun gaza cin
kungiyar Alaves a gida. Wasanni sama da 50 kenan a jere kullum sai Real Madrid
ta jefa kwallo.
Ku
na da labari cewa FIFA ta Duniya ta dakatar da babban dan wasan nan na kasar
Argentina Lionel Messi da ke Barcelona. Dan wasan gaban ba zai buga wasanni 4
ba bayan an same sa da laifin fadawa Alkalin wasa maganganun da ba su dace ba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment