Sunday, April 9, 2017

Ga wasa ga aiki: Dan kwallo yayi digirgir

Dan wasa Chiellini ya kammala Digirin sa na biyu


– Babban Dan wasan kwallo Girogio Chiellini ya kammala karatu a Jami’a


– Dan wasa Chiellini yayi karatun Digirgir a Jami’ar Turin


– Chiellini rikakken Dan wasan baya ne a Kungiyar Juventus




Mun samun labarin cewa shahararren dan wasan kwallon kafar nan mai suna Girogio Chiellini ya kammala karatun sa a Jami’a. Wannan dai ya nuna cewa ashe cin danko ba sai kaza kurum ba.

Babban dan wasan bayan ya kammala karatun Digirin sa na biyu a fannin harkar kasuwanci watau M. BA. Dan kwallon yayi karatun ne a Jami’ar Turin ta kasar da ke cikin Birnin da Kungiyar Juventus ta ke.


Babban dan wasan mai taka leda ya ba Jama’a mamaki inda ya zama cikin wadanda su ka fi kowa hazaka a aji. Chiellini yayi nazari ne a kan Kungiyar sa ta Juventus inda babban Farfesan nan Pietro Paolo Biancone ne ya duba aikin sa.

An dai ce bikin Danjuma ba ya hana na Dan-jummai, yanzu haka Juventus na da wasa da Kungiyar Chievo a wannan mako.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...