– A rana irin ta yau aka kashe Malam Ja’afar Mahmud Adam
– Wasu suka kashe babban Malamin yana tsakiyar sallar asuba
– Sheikh Ja’afar yana cikin manyan Malaman da aka yi a Arewa
A dalilin tunawa da Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Daura da
aka kashe shekaru 10 da suka wuce nayi wannan rubutu. An dai
kashe Malam Ja’afar yayin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin da yake
Limanci.
Har yau dai ba a kama wadanda ke da hannu wajen kashe babban
Malamin ba wanda ya ba addini rayuwar sa. An dai haifi Malam Ja’afar a Garin
Daura a gidan Malamai, nan ya fara karatun addini daga nan ya koma Kasar Kano
inda yayi almajiranci.
Daga nan ya kara karatun addini da boko a Garin Kano har ya samu nasara a gasar
karatun Al-kur’ani. Daga nan Malamin ya samu wucewa Kasar Saudiyya inda ya
Digiri a fannin Ilmin Al-Kur’ani a Jami’ar Madina.
Bayan ya kammala kuma ya zarce Kasar Sudan inda ya samu Digiri na
biyu a fannin yaren larabci. A lokacin da aka kashe Sheikh Jafar yana digirin
sa na uku a fannin addini Musulunci a Jami’ar Danfodiyo ta Sokoto.
Marigayi Ja’afar yana cikin malaman da suka kware wajen tafsirin
Al-kur’ani da kuma iya bayani dalla-dalla ga Jama’a bisa koyarwar Sunnah ta Manzon tsira SAW. Malam
Jafar ya koyar da al'umma ilmi da dama na Tauhidi da Hadisi da Sira da Fikihu
na tsawon lokaci a fadin kasar nan.
Allah ya jikan Malam Jafar Adam da Albani-Zaria ya karbi shahadar su. Ameen.
Muhammad Malumfashi ya rubuta wannan a shafin NAIJ Hausa jiya
No comments:
Post a Comment