Ikon Allah: Wani kare ya
hana a tada bam
kare yayi sanadiyar cecen
rayuwar mutane masu dinbin yawa a Garin Borno inda ya hana wata yarinya tada
bam a wani gidan biki
Sai ace
ko karen nan yayi mutuwar shahada kenan inda ya rasa ran sa yana kokarin kare
na Jama’a? Wannan kare dai yayi sanadin karin kwanan mutane masu yawa yayin da
ya hana wata yariniya harba bam a wani gidan biki.
Mun samu
labari cewa wannan kare na wani mai gida ne a kusa da inda wannan abu ya faru.
Karen dai ya hana wata ‘yar yarinya kutsawa cikin Jama’a domin ta harba bam
wanda da ya ga bayan mutane da dama a cikin wani gida da ake sha’anin biki.
Jami’an
‘Yan sanda su ka ce ko da karen ya hango wannan yarinya ta auka cikin Jama’a
sai ya bi ta, nan fa aka yi ta kaya-kaya har bam din ya tashi, nan ne aka rasa
wannan kare. Wannan abu dai ya faru ne a Garin Belbelo da ke Jihar Borno.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment