Mai kudin Duniya bai bari yaran sa su rike wayar salula sai sun girma
–
Attajirin Duniya Bill Gates yace bai barin kananan ‘ya ‘yan sa su mallaki waya
– Bill Gates yace sai sun girma
yake ba su damar samun tarho
– Bill
Gates dai yace agogon hannun sa bai wuce Dala 10 ba
Tun shekaru 23
da suka wuce Bill Gates yake cikin Attajiran Duniya to sai dai duk da haka
agogon da yake daurawa bai wuce Dala 10 rak ba kamar yadda NAIJ.com ta samu
labari daga wata Jaridar Amurka.
Bill Gates da
matar sa Melinda suna da ‘ya ‘ya 3 ne rak a Duniya inda babban ke da shekaru
20. Mr. Gates yace bai bari yaran su taba rike waya sai sun kara girma sun kai
shekara 14. Bill Gates ne dai wanda ya kirkiro manhajar Microsoft a Duniya.
Mai kudin
Duniyan yake cewa kuma ba kasafai yake bari yaran su rike waya ba a ko da
yaushe musamman cikin dare lokacin barci. Bill Gates yace hakan zai taimaka masu
kwarai da gaske a rayuwar su.
Duk Duniya a wannan shekarar
ma dai kasurgumin Attajirin ne ya fi kowa kudi a Duniya. Arzikin Bill Gates ma
dai karuwa yayi daga Dala Biliyan 75 zuwa Dala Biliyan 86 a bana. Duk da haka
Bill Gates bai wasa da tarbiyyar iyalin sa.
[NAIJ Hausa]
Instagram Takipçi Satın Al
ReplyDeleteToptan Telefon Kılıfı
Resimli Magnet
Silivri Çatı Ustası
Çerkezköy Çatı Ustası
MVQ
salt likit
ReplyDeletesalt likit
dr mood likit
big boss likit
dl likit
dark likit
J5JY