Makonni kusan uku kenan ba a
ga Buhari a taro ba
– Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai halarci taron FEC ba
– Yanzu
haka Osinbajo ke jan ragamar taron
–
Makonni uku kenan ba a ga shugaban kasar ba
Kusan makonni uku kenan ba a ga shugaba Buhari a taron
Majalisar FEC da aka saba yi kowane mako ba. A halin yanzu
haka Mataimakin shugaban kasa Farfesa YemiOsinbajo ke jan ragamar taron da ake
yi na yau.
Wancan makom da ya wuce
ba ayi taron ba sam, inda shugaban kasar yace lokacin an dawo daga hutun Easter a kurarren
lokacin don haka aka bari sai Ministoci sun kintsa tukun ta bakin Malam Garba
Shehu.
A makon baya ma dai shugaban kasa bai halarci taron ba
inda Mataimakin sa ne ya ja ragamar. Ministan yada labarai yace ba wata matsala
ce ta sa hakan ba illa-iyaka shugaban kasar ya ba Farfesa Yemi Osinbajo domin
ya cigaba da wasu ayyuka na dabam.
Kwanaki aka kori wani
Dan jarida daga Fadar Villa mai suna Olalekan Adetayo bayan Dan jaridar ya
bayyana cewa shugaban kasar bai lafiya ba kuma a ganin sa. A taron na yau dai
akwai wanda ta maye gurbin Babachir Lawal watau Dr. Habiba Lawal.
Yanzu haka mu ke jin cewa Ministan yada labarai na kasa Lai Mohammed yace shugaba Buhari na bukatar hutu don haka daga gida zai rika aiki.
Allah Ya kyauta Na gaba. Allah Ya qarawa shuwagabanin mu lafia da kuma Jagoranci Na alkhairi.
ReplyDelete