HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA
Huduba kan Aure-Daga Bakin Imam Dr. Saeed Muhammad Yunus
Assalamu Alaikum wa Rahmatul Lah,
Godiya ta tabbata ga Allah SWT wanda ya halitta mu daga rai guda. Muna
shaida cewa babu abin bauta da gaskiya face Allah dai shi kadai, ba shi da ‘da
ko mata ko tamka ko wani abokin tarayya ko mataimaki. Muna kuma shaida cewa Annabi
Muhammad SAW, Bawan Allah ne kuma Annabi wanda ake koyi da Shi, tsira ta
tabbata gare Sa da Alayen sa da Sahaban sa da wanda su ka bi tafarkin Su.
Jama’a mu kiyayi Allah mai girma mu ji tsoron Sa, mu kuma guji saba masa
alhalin muna sane. Daga cikin abubuwan da Musulunci ya jawo hankalin Jama’a
akai da kiyayewa shi ne abin da ya shafi Auratayya. Auratayya abu ne da ya
shafi zamantakewa na Duniya da kuma Addini. A cikin aure akwai hikima
madaukakiya da amfani bi-la-adadin da kuma ma’anoni manya-manya. Wani abu ne na
tilas domin kuwa da shi ake gina gida da al’umma kuma da shi ne ake samun
daukaka kuma a rufe idanuwa da farji. Da auratayya ne ake kara yawa, yayin da
wani ya fita sai wani ya shigo. Ai aure ya isa ka ga aya daga ayoyin Allah, ai
aure ayar Allah ce! Allah SWT yana cewa: Daga cikin ku Allah ya halitta maku
matayen ku, domin ku samu natsuwa da soyayya da tausayi. Allah yace hakan
lallai aya ce ga masu tunani. Allah ka sa mu cikin masu tunani.
Addinin Musulunci ya buga wani misali mai ban sha’awa da mamaki wanda ya
nuna cewa ana samun aure ne ta hanyar iyaye kuma lallai a nemi albarka a cikin
auren wajen sauwake shi. Daga ciki akwai wani hadisi da Imamu Ahmad da Bayhaqy
su ka fitar daga bakin A’isha mai gaskiya ‘yar mai gaskiya RA tana cewa mafi
albarka game da mata da kuma mafi girma ga mata su ne wadanda ba a wahala ba
wajen auren su, watau ba a wahalar da mutum ba; ya samu sauki wajen auren su.
Mu sani cewa wadanda ke wahalar da Jama’a, su ke daura nauyi game da auratayya,
su na sabawa tsari na shari’a na Allah da Manzon sa Annabi SAW. Ya ‘Yan uwa ku
sani cewa ya halatta Mace tace da Namiji tana son sa kamar yadda ya halatta Namiji
ya ce yana son mace wanda shi ma ya fi sauki (dama Namiji an san shi wanda bai
jin kunya ba, (ba wai bai da kunya ba)). Kuma don Mace tace da Namiji tana son
sa, wannan an gani a lokacin Manzon Allah SAW wanda wata tace tana son Sa, amma
dai bai ce bai so ba, sai ya nema mata wani Mijin. A takaice ya ku iyaye, ya
halatta ku nemawa ‘Ya ‘yan ku Mata ko Maza, amma idan har wata ko wani tace ko
yace ba ta ko ya so, don Allah ka da a matsa sai an yi aure, domin wannan yana
haifar da fitina da bala’i iri-iri a doron kasa. Idan mutum yace bai son wani
sai a hakura, aure dai ba za ayi ba! Domin Manzon Allah ya dukar da kan sa; don
ba a san abin da zai biyo baya ba.
Akwai wasu matsaloli da su ke faruwa a yanzu wanda ya kamata a jawo hankali
a game da su; matsala ta farko ita ce samari sun zama dika-dika, sun ki aure
sun tsaya su na kakalo wasu abubuwa da ba su cikin Al-Kur’ani ko Sunnah, sai ka
ga mutum ya cika shekara 40 bai yi auren fari ba. Ana makalewa da wasu dalilai
marasa amfani yayin da Ubangiji SWT yace idan har kun yi aure don Allah kuna
talakawa zai azurtaku daga cikin falalar sa (A cikin Suratun Nur). Abdullahi
Dan Abbas yana cewa: Ku nemi wadatuwa cikin aure watau Idan ka na son kudi, sai
ka yi aure. Amma fa ban fada maku cewa Hadisi ne na Manzon Allah SWT ba! Ban ce
da ku Hadisi bane! Magana ce ta Dan Abbas wanda Sahabi ne da imanin sa ya cika
har ya batse. Akwai wani Hadisin karya da ake cewa idan talauci ya addabi mutum
to ya kara aure, to ai kuwa za ka kara talauci, ka kara lalacewa! Allah ka
shiryar da mu!
Abubakar As-Sadiq RA babban Sahabi kuma Abokin Manzo SAW yana cewa Mutane:
Ku bi Allah ku bi abin da ya umarce ku a cikin auratayya sai ya cika maku
alkawarin ku. Kun ji Maza! Yace idan har kun bi Allah, zai cika maku alkawari.
Ya ku ‘Yan Uwa akwai wadanda kuma kudi su ke nema da auren watau auren jari; ba
za a nemi kowa ba sai ‘Yar mai kudi. Annabi SAW wanda ba ya karya yace duk
wanda yayi aure don kudi, to karshen sa Talauci. Haka nan duk wanda ya dubi
kyau kurum wajen aure wata rana zai ga matar ta kare mummuna har ta zama bai
kaunar ganin ta-Akwala! Amma duk wanda yayi aure domin addini Allah Madaukaki
zai cika masa burin sa. Amma Addini kuma bai hana idan mutum ya ga wata mai
kyautatawa mutane kuma kyakkyawa ya aura ba, asali ma addini ya ba da dama ne.
Daga cikin matsalolin da ake fama da su a yau shi ne rashin daraja masu addini,
ana hana mata su auri mutanen kirki. Alhali fa Annabin Rahama SAW yana cewa duk
wanda ya zo maku (neman aure), kuma ku ka yarda da halin sa da addinin sa to ku
aura masa. Wadannan sharuda 2; ko da mutum yana kwana a masallaci amma bai da
halin kirki bai cancanta ba, haka-zalika akasin haka. Amma fa ku sani cewa babu
kamala sai Allah Mai Girma, domin ka da a ce ai yana da ‘yar matsala kaza a
hana sa, kowa kuwa yana da ‘yar matsala. Allah ka shiryar da mu! Annabi SAW
yake cewa idan ku ka ki aurar masa, za a samu fitina da barna da yawa a doron
kasa, Tirmidhi da Ibn Majah da Hakim su ka fitar da wannan Hadisi da sanadi mai
kyau.
Akwai wasu daga cikin Iyaye; Allah ya shiryar mana da su da ke cin amanar ‘Ya
‘yan da Allah ya dora masu. Su na hana ‘Ya ‘ya su auri wadanda su ka dace da
su; Yarinya tayi karatu amma sai su aurar da ita ga wani ma-ci amana, su na
neman mukami da matsayi da darajar wannan mutumi sun manta da darajar da Allah
ya ba su. Daga cikin Iyaye akwai makwadaita wadanda su ke maida ‘Ya ‘yan su
wasu kayan kasuwanci; ana cewa waye ya zo? Shin ya zo da mota? Wace irin mota?
Allah ka shirye su! Wannan babban bala’i ne! Ina rahama ga wadannan iyaye da ba
su tunanin aurar da Diyar su ga wanda bai da addini ba? Jama’a ina za mu je ne?
Lahira fa za a tafi!
‘Abubuwan da ya zo mana a wannan zamani shi ne za a iya ba Likitocin mu
dama su binciki lafiyar Ma’aurata. Domin musamman a auren zumunci a kan gaji
rashin lafiya wanda wannan Littafin Tib-An-Nawawi ya tabbatar’. Ba mamaki a
cikin zumuntar nan a samu cuta irin ta Sikila don haka Likitoci amintattu su yi
bincike. Har da kuma sauran cututtuka na bala’i irin su Kanjamau. Ba haramun
bane yin bincike wajen aurar da Budurwa ko Bazawara. Allah mu ke roko ya
shiryar da mu da zuriyar mu!
Huduba ta biyu tana cewa bayan godiya ga Allah da yabo ga Annabin mu SAW
wanda yake cewa yin aure na cikin Sunnar sa. Allah ka kara daraja ga farin
Jakada Annabi Muhammadu SAW. ‘Yan uwa mu kara godewa Allah Ubangiji, a yau muna
ganin abubuwa na lalata su na faruwa ga ‘Ya ‘yan Musulmi masu tsari. Wa ya
haifar mana wannan bala’i kafin aure da bayan aure? Ya ku Al’ummar Manzon Allah
SAW ku sani cewa da dama sun bar Sunna yayin da za su yi aure; ba a yin aure
yadda Sunna tace; kawai ana haduwa ne yadda aka ga dama. Wannan yana haifar da
fitina. Kuma ana yin barna wajen aure tare da almubazzaranci da alfahari da
nuna an-isa, wanda hakan na sa Allah yayi fushi. Abincin da ake zubarwa a rana
guda, na rantse da Allah sai wasu mutanen su samu na cin wata gudu. Abu na uku
kuma shi ne cakuduwar maza da mata da kuma yadda Amarya da Ango ke fitowa gaban
mutane; ka ga macen kirjin ta (har ma da sashen nonon ta) a waje a gaban wasu mutane
sha’awa. Amarya tana rawa a gaban wani Makadi rike da hannun Angon ta. Jama’a
ina koyarwar Annabi Muhammadu SAW? Idan abin ya cika, sai ka ga an kashe kudin
gaske wajen haskawa a Talabijin. Sannan kuma ka ga ana daukar hotuna na haram
wanda ba abin da wannan yake haifarwa sai fitina! Daga ciki akwai wasu wasanni
na banza da ake yi; akwai wani zama na Party
‘Till-Dawn’ har gari ya waye a sa’ilin da Bayin Allah na kwarai ke neman
gafarar Allah Madaukaki. Allah Tabaraka Wa Ta’ala yace su na neman gafara ga
wasu can kuma su na ta lalata. A dalilin bikin aure sai a bar sallolin da aka
farlanta don wai rana guda! Abu na biyar kuma, a kan cire rigar kunya. Ita ce
kadai ranar da ake warewa Shaidan amma ban da ita kullum ta Allah ce, amma a
ranar dai sai a dan huta; rai dangin goro. Ka ga an sa motoci da babura su na
kara, ana tukin ganganci, wai duk ana murnar auratayya. Abu na karshe watau na
bakwai shi ne cutar da samari da ‘yan mata da kowa game da abubuwan da ake ji
na sauti a cikin Unguwanni da ke hana mutane ambaton Allah kuma yana jawo
fitina a doron kasa.
‘Yan uwa wadannan abubuwan su na cikin abin da su ka jawo wasu matsaloli da
mu ke fuskanta a yau. Daga cikin matsalolin da ake samu shi ne sai ka ga mata
na tafiya tsirara; idan har ka yi magana sai a fada maka cewa ‘Ai Imani yana
zuciya!’ Mata na cin amanar Mazajen su, su na rashin da’a ga Allah. Ubangijin
Ka na nan a madaka! Lallai Ubangijin Ka bai manta ba!! Al’ummar Musulmi sun
shiga rudu an manta da tafarkin Allah; sai ka ga yaro na tuka babur bisa titi
yana goge tayan baburin dsr, sai ka tambaya ka ji ya aka yi a Ranar aure. Abu
na uku kuma shi ne rashin ba iyali hakkin su na ciyarwa da sauran su; sai ka ga
daga an yi albashi mutum ya raba kudin sa ga matan banza wadanda yake kwanciya
da su ba matan sa ba. Wannan yana kawo bala’o’i wanda an bar hanya tun kafin
aure. Ga batun sake-sake; daga yaro ya balaga ko bai da sana’a sai ace za ayi
masa aure, kuma Jama’a su yarda. A kafin ranar aure a sabawa Allah haka a ranar,
ga shi nan an haifi bata-gari. Daga cikin Manyan mu kuma sun goyi baya; ku dubi
yadda Majalisar Dattawar da ya kamata su zama masu kafa doka su ke goyon-bayan
wannan barna. Allah ka shirya su kuma Allah yana kallon ku Dattawa! Ko ku cika
alkawarin da ku ka yi ko kuma Allah ya kama ku! Ban ce dukkanin su ba amma ku
tuba don kuwa kun ci amanar Manzon Allah da al’umma kaf don kuwa zaben ku aka
yi, amma a dalilin wani son zuciyar ku kun saba. Wai sai ace mutum guda ne ko
10 za su gyara kasa? Su suka hana ruwa gudu, ga masu tuki a kan hanya ba su da
hankali. Wanda ba Likita ba yayi karyar Likitanci. Wanda ba Malami ba ya bude
Makaranta! Kasa kuma tayi shiru. A ce mutum daya yayi gyara. Kai! Komai ka gani
kurum hauka ne! Jama’a duk wannan matsalar ba komai ya jawo mana su ba Wallahi
Auratayya ce; kar ka raba daya biyu; da aure yayi kyau, da abubuwa sun yi kyau.
Lokaci ba zai bamu damar mu fadi irin abin da auratayya ta haifar na kirki ba.
A haka za a haifi fitinanne, ya kuma tafi Majalisar ya zama Dan kuka. Allah ya
shiryar da mu!
Abin da ya jawo aka wulakanta auratayya tun farko shi ne an bar Malamai na
Allah an koma ga Malaman Duniya wadanda ba su ba da fatawar komai sai shirme.
Dole mu yabi wadanda su ka bi hanyar Allah da Manzon Sa wajen Auratayyar su,
Allah ka taimake su. Daga karshe muna ta’aziyyar babban Malamin Al-Kur’ani da
ya rasu a Kano shekaran jiya watau Dakta Alhassan Sa’eed Jos. Allah ka masa
rahama ka haskaka kabarin sa ka za ya zama dausayi na Aljanna ka sa Aljanna
makoma ka cika burin sa ga Iyalin sa. Allah ka mana rahama gaba daya don mu ma
muna tafe. Allah ka azurta mu da aminci a Najeriya ka taimaki dukannin Shugabannin
mu. Allah ka karawa Shugaba Buhari lafiya da daukaka ka kuma gusar da damuwar
sa da Makiyan sa ka watsa su. Allah ka sa mu cikin Bayin kwarai ka kuma taimake
Musulmai da Musulunci. Allah duk wanda ba su da aure a cikin masallacin nan da
wajen masallacin, Allah ka ba su, masu son karawa idan har alheri ne, Allah ka
ba su dama! Ya Allah muna rokon ka wadanda su ka rasa maza ka ba su. Allah ka
kawowa masu neman aure na kirki!
Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba.
(Malam ya gabatar
da wannan huduba tun kwanaki, ban samu damar buga ta ba)
Twitter: @Ya_waliyyi
Denizli
ReplyDeleteKonya
Denizli
ısparta
Bayburt
VV5O8J
Sakarya
ReplyDeleteKayseri
Van
Konya
Samsun
O2H5H
goruntulu show
ReplyDeleteücretli
G4O716
hakkari evden eve nakliyat
ReplyDeleteankara evden eve nakliyat
muğla evden eve nakliyat
elazığ evden eve nakliyat
erzurum evden eve nakliyat
LKDJK
sivas evden eve nakliyat
ReplyDeleteerzurum evden eve nakliyat
bitlis evden eve nakliyat
mardin evden eve nakliyat
rize evden eve nakliyat
0CE