Siyasa:
Matsalolin da Jam’iyyar APC ke fama da su
– A cikin makon nan ne Gwamnatin Buhari ta shekara biyu da kafuwa
–
Sai dai har yanzu Jam’iyyar APC ba ta samu alkibla ba
– Kamar dai PDP, Jam’iyyar mai
mulki tana cikin rikici
Jam’iyyar
APC na fama ta zama Jam’iyya mai mulki tun kafuwar Gwamnati. Shugaban
Jam’iyyar da kan sa ya bayyana cewa ba haka su ka so ba. Ko
daga ina aka samu matsala a Jam’iyyar? G
- 1. Rashin kudi
Jam’iyyar
APC na fama da matsalar rashin kudi tun bayan hawan Shugaba Buhari mulki wanda
ya toshe duk wata kafa da Jam’iyar za ta rika tatsa daga Gwamnatin Tarayya.
2.
- Nadin Shugaban kasa
Shugaban
Jam’iyyar Cif John Oyegun ya bayyana cewa Jam’iyyar ba ta jin dadin irin nadin
da Shugaban kasa yake yi. Mafi yawanci ba a tuntubar Jam’iyya da ‘Ya ‘yan ta.
Sannan kuma har yanzu ‘Yan PDP na nan rututu cikin wannan Gwamnati rike da
matsayi ba a sauya su ba.
- . Rikicin Majalisa da sauran na cikin gida
Tun
wajen nadin Shugabannin Majalisa Jam’iyyar APC ta fara dabawa kan ta wuka a
ciki. Yanzu dai kusan aikin gama ya gama kuma ana yi wa juna kallon doya da
manja ne.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment