Uwargidan
Gwamnonin Arewa da inda su ka yi karatu [Cikin Hotuna]
– Mafi yawan Gwamnonin Arewa su na da ofisihin Uwargida na iyalan su
–
Sai dai wasu Gwamnonin ba su jefa matan su cikin harkar shugabanci ba
–
Ga dai kadan daga cikin matan Gwamnonin Arewa maso yamma
Mun kawo maku hotunan matan Gwamnonin Arewa. Irin su Gwamna Ibrahim
Geidam dai ba a san matar sa ba. Don wasu Gwamnonin ba
su bari matan su su shiga cikin sha’anin mulki
1.
Matar
Gwamnan Jihar Adamawa: Hajiya Maryam Muhammad Umar Jibrilla
Matar Gwamnan Jihar
Adamawa ‘yar gidan Sani Zangon-Daura ce wanda fitacce ne a Katsina da Najeriya.
Tayi karatu har Digir-gir a Kasar Birtaniya.
2.
Matar Gwamnan
Jihar Bauchi: Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar
Abin da zai burge ka shi ne tun shekarar 1979 ta auri Mijin
ta wanda yanzu ya zama Gwamna. Tayi Digiri har 2 a Jami’ar Ahmadu Bello ta
Zariya.
3. Matar Gwamnan Jihar Borno: Hajia Nana Kashim
Shettima
Ana mata lakabi da Uwar Marayu ita ma tayi karatu a Jami’ar
Maiduguri kamar dai Mijin ta Kashim Shettima.
4. Matar Gwamnan Jihar Gombe: Hajia Adama
Dankwambo
Uwargidar Mai girma Gwamna Dankwambo na Jihar Gombe kuma tana
bakin kokari wajen dafawa Mijin ta.
[NAIJ.com]
No comments:
Post a Comment