Karamar magana ta zama babba: Ahmed Musa ya angonce da Juliet Ejue
– Babban Dan wasan Super Eagles Ahmed Musa ya auri Juliet
– Dan wasan na Najeriya ya saki
matar sa kwanaki
– An ji cewa matar tace sam ba za
ta zauna da kishiya ba
Da alama Ahmed Musa ya auri sahibar sa Juliet. Dan
wasan mai shekaru 24 ya shiga daga ciki. Kwanaki
dai ya rabu da matar sa Jamila.
Ko
ka dai har yanzu ba mu samu tabbaci ba amma ba mamaki babban dan wasan gaban
Super Eagles Ahmed Musa ya auri Sahibar sa Juliet Ejue. Mun dai ga wasu hotuna
da takwarar sa 'dan wasan Najeriya Juwon Oshinawa ya dora na yawo da ke nuna hakan.
Kwanaki
dai Ahmed Musa ya rabu da uwar ‘ya ‘yan sa bayan yayi niyyar kara mata inda ta
tubure tace ba za ta sabu ba. Mun ji cewa dai sun rabu bayan ya ba ta kyautar
wata katuwar mota da gida a Kano.
Tun
a Kano dai Ahmed Musa ya hadu da Jamila sai dai yanzu ya zama Angon Juliet wata
mutumiyar Garin Kalaba na Jihar Kuros-Riba. Musa dai ya sayawa Juliet gida a
Lekki da ke Legas da kuma zugegiyar Marsandi.
No comments:
Post a Comment