Friday, May 12, 2017

‘Yar Najeriya mai shekaru 63 ta haihu



Wata mata mai shekara sama da 60 a duniya ta haihu 



Wata mata mai shekaru 63 ta haihu bayan shekaru 38 babu haihuwa


Hakan ya sa ta zama uwar jinjirar da ta fi kowa tsufa a Afrika


– Wannan abu dai ya faru ne a Najeriya




Duniya dai kullum ka ga abin mamaki. Kwanaki wata Yarinya mai shekara 10 ce ta haihu a Kasar Kenya Yanzu kuma wata tsohuwa ce mai shekara sama da 60 ta samu karuwa.

Mun samu labarin wata mata dattijuwa ‘yar shekara 63 da ta samu karuwa. Duk da shekarun wannan mata yanzu Ubangiji ya nufa ta haihu lahiya kalau. Hakan ya sa ta zama duk Afrika babu wanda ya taba haihu da irin wannan shekaru.

Wannan mata Margaret Davou tayi ritaya tuni daga aiki a Garin Jos ta kuma yi shekaru 38 babu haihuwa sai wannan karo aka dace inda aka yi amfani da kimiyya. An dai dasa ruwan haihuwar ne a kwalba kafin a maida sa cikin sa har ta haifi diya mace.

Kwanaki wata karamar yarinya mai shekara 10 da haihuwa a duniya ce ta haifi wata itama. Wannan abin al’ajabi ya faru ne a Kasar Kenya a shekaru biyu da su ka wuce.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...