Champions
League: Juventus za ta kara da Real Madrid a wasan karshe
– Wannan karo ma dai Kungiyar Real Madrid karasa zagayen karshe a gasar Champions League
– Real Madrid na iya kafa tarihin
da ba a taba ba
– Babu kungiyar da ta taba cin
kofin sau 2 a jere
Duk
da Real Madrid ta sha kashi a hannun makwabtan ta Atletico Madrid ta isa wasan
karshe. Watakila
Real Madrid din tayi abin da ba a taba yi ba bana. A
shekarar 98 dai Real Madrid ta doke Juventus a wasan karshe.
An
dauki shekaru da dama babu Kungiyar Kasar Italiya da ta dauki kofin UEFA
Champions League na zakarun Nahiyar
Turai tun bayan AC Milan. A wata fafatawa da aka yi a 1998 dai Real Madrid ta
doke Juventus a wasan karshe.
Bara
dai Real Madrid din ce ta dauki kofin ko wannan karo za ta bar tarihi tayi abin
da ya gagari kowa na daukar kofin sau 2 a jere. Atletico dai ta doke Real
Madrid a wasan da ci 2- 1, sai dai wannan bai yi tasiri ba don Real Madrid
din tayi nasarar 3-0 a wasan farko.
Jiya
kun ji cewa Juventus ta isa zagayen karshe a gasar UEFA
Champions League na zakarun Nahiyar
Turai bayan ta doke Monaco ta Faransa da ci 2-1. A zagayen farko Juventus tayi
nasara da ci biyu da nema.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment